Assalamu alaikum,

Wannan Shine Cikakken Karatun Al-Kur’ani Mai Girma Na Sheikh Jafar Mahmud Adam RahimahuAllah. Kada a manta a ziyarci wannan shafin domin samun cikakken tafsirin iOS version wato mai aiki kan wayoyin iPhones da iPads.

Application din Yana Da Nauyin 1.2GB Amma matukar mutum zai sayi waya Data Tasamma sama Da Dubu Goma To yakamata ace Akwai Tafsirin Littafin Allah Subhanahu Wata’ala aciki. Allah Ya Shiryar Damu Ya Kuma Datar Damu Ameen.

Akwai Ayoyi Guda 13 Kamar Haka Da Muka Nemi Tafsirinsu Bamu Samuba: Ayoyin Suratu Yunus 16,17 da 18, Ayoyin Suratu Ibrahim 01 zuwa ta 09 Da Kuma Suratu Yasin Aya ta 30.

Idan Kuna Da Tafsirin Wadannan ayoyi saiku Aikomin a Email Dina kareemtkb@gmail.com zanyi kokari na sakasu cikin wannan manhajja In Shaa Allahu.

A Duk lokacin Da Kuke Bukatar Wannan Tafsiri Domin Wayoyin Ku Bude Shafin Kareemtkb.com Kuzo Wannan Shafi saiku Danna Link Da Kukeso Domin Saukewa.

Muna Bidar Addu’arku Ta Alkhairi. Allah ya karba mana wannan aiki Damu Da Ku Baki daya.

Ku Danna Alamar Saukewa Domin Sauke Wannan Tafsiri Na Alkurani Mai Girma na Malam Jafar. Mai Jan Bakin Shine Malam Sa’idu Haruna.

YADDA ZAKU SAUKE TA HANYAR AMFANI DA COMPUTER:

Idan kuka danna DOWNLOAD toh zai kaiku shafin Google-Drive inda zaku sake danna Download domin sauke APK din. Bayan kun sauke sai kuje inda yake akan computer dinku saiku aikashi zuwa wayarku kirar Android ta hanyar amfani da USB-CABLE. Daga nan saiku bude wayarku kuje inda APPLICATION yake saiku danna domin yin Install. Akwai Bukatar kuje settings a wayoyinku domin kunna INSTALLATION FROM UNKNOWN SOURCES.

YADDA ZAKU SAUKE TA HANYAR AMFANI DA WAYA:

A wayoyin kuma bayan kun danna Download, saiku zabi Google-Drive kamar yadda ya bayyana a hoton dake biye:

IDAN KUNA DA SAMA DA EMAIL DAYA AKAN WAYAR SAIKU ZABI WANDA KUKESON ACCESSING GOOGLE DRIVE DASHI SAIKU DANNA OK

SAIKU DANNA “PACKAGE INSTALLER”

YANZU GA APPLICATION DIN YANA SAUKA AKAN WAYARKU

Daga nan sai kuje inda ya sauka akan memory na wayarku saikun danna kuyi installing nasa. Kada a manta a bada izini ga Unknown-Sources a settings saboda wasu wayoyin basa barin install na application wanda ba daga play store yake ba.

Idan kun fuskanci wata matsala wajen saukewa ku tabani a kareemtkb@gmail.com

Idan kun sauke kuma kunyi install ga yadda app din yake daga ciki:

Haka Zalika Akwai Wannan Tafsiri Cikin Dandalin APPSTORE ga wayoyin iPHONE da Kum iPAD. Ku Danna Link Dake Kasa Domin Saukewa a wayoyinku Kirar Apple.